Labanan na neman kwantar da boren ′yan kasar | Labarai | DW | 21.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Labanan na neman kwantar da boren 'yan kasar

Majalisar gudanarwar kasar Labanan, za ta koma zama na gaggawa bayan fahimtar da ta yi na tasirin zanga-zangar da 'yan kasar ke yi wadda ake ganin kasar ba ta taba ganin irinta ba.

Masu zanga-zangar adawa da matakin tsuke bakin aljihun da gwamnatin Labanan din ta dauka, na ci gaba da karfi ne daidai lokacin da suke shiga rana ta biyar da mamaye manyan titunan kasar.

Mahukunta dai sun ce za su yi kokarin sassauta sauye-sauyen da suka bullo da su musamman hareje-hareje da nufin bunkasa samun kudade na shiga, don mika wuya ga bukatar ‘yan kasar da ke cewa gwamnatin Firaminista Saad Hariri ta kai su iya wuya.

Masu boren sun datse manyan hanyoyin da ke Beirut babban birnin kasar, yayin da su ma makarantu da sahguna gami da bankuna ke garkame.

Kokarin da gwamnatin ta Hariri ke yi, shi ne samar da yarjejeniya tsakaninta da bangarorin da take huldar arziki da su dangane da sabon tsari na haraji a kundin kasafin kudin kasar na badi. Amma masu boren sun nace kan sai shugabannin su yi murabus.