1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Beljiyam: Kokarin gyara alaka da Kwango

June 8, 2022

Sarki Philippe na kasar Beljiyam, ya karrama wani sojan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ya fafata a yakin duniya na biyu. Sarkin ya kuma kai ziyara kushewar 'yan mazan jiya, inda ya dora furanni a kan dogon yaro.

https://p.dw.com/p/4CR27
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Ziyarar Sarki Philippe na Beljiyam | Ganawa da Shugaba Felix Tshisekedi
Sarki Philippe na Beljiyam ya gana da Shugaba Felix Tshisekedi na KwangoHoto: Nicolas Maeterlinck/Belga Photo/AFP/Getty Images

Wannan dai na cikin ziyarar kwana shida da sarkin Philippe na Beljiyam din ya fara da zummar gyara alakar diflomasiyya a tsakaninsu da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, bayan ta'asar da ake zargin kasarsa ta yi wa Kwangon a zamanin mulkin  mallaka. Mulkin mallakar da kasar Beljiyam ta yi wa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, na cikin masu tsauri da kasashen Turai suka yi wa galibin kasashen Afirka a karni na 19 zuwa karni na 20. Masana tarihi na kiyasin cewa miliyoyin mutane ne aka kashe a zamanin rainon da Beljiyam ta yi wa Kwango, inda yunwa da cututtuka suka yi wa al'ummar kasar lahani.

Karin Bayani: Mulkin kaka-gida a nahiyar Afirka

To sai dai Firaministan Beljiyam din Alexander De Croo da ke cikin tawagar Sarki Phillippe wacce ke ziyara a Kinshasa ya ce, sun ziyarci kasar ne da zummar kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu. Ziyarar Sarkin na Beljiyam dai na zuwa ne shekaru biyu bayan da ya rubutawa shugaban kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon Felix Tshisekedi wasika, inda ya nuna damuwarsa a kan abubuwa marasa dadi da suka faru a zamanin mulkin mallaka. Sai dai duk da cewa kawo yanzu tawagar Sarki Phillippe na Beljiyam ba ta kammala ziyarar tata ba, galibin al'ummar kasar Kwango su miliyan 90 na fatan sarkin zai yi amfani da ita ya fito karara ya nemi afuwarsu a game da zargin cin zalin da aka yi musu a lokacin mulkin Sarki Leopold. 

 Ziyarar Sarki Philippe na Beljiyam a Kwango
Sarki Philippe na Beljiyam, na kokarin farfado da alaka tsakanin kasarsa da Kwango Hoto: Nicolas Maeterlinck/dpa/BELGA/picture alliance

Babban abin da ziyararta Sarki Philippe ta mayar da hankali a kai shi ne, kokari na faranta wa al'ummar Jamhuriyar Dimukuradiyyar ta Kwango rai, ta hanyar mika kayan tarihin kasar da Beljiyam din ta sace musamman hakorin Patrice Lumumba ga gwamnati. Lumumba dai shi ne firaministan Kwango na farko bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960, kuma kafin zamansa firaminista ya kasance gaba-gaba wurin jagorantar gangamin korar mulkin Turawa a kasarsa. To sai dai jim kadan bayan ya hau karagar mulki, wasu 'yan awaren kasar tare da sojojin haya na Beljiyam suka kashe shi.

Karin Bayani: Cin zarafin mata a Kwango da Afirka ta Tsakiya

Hakan ce dai ta sanya kusoshin gwamnatin Kwango kamar Théodore Omekenge ke cewa, Beljiyam ta nuna alamun tausar 'yan kasar daga tabargazar da aka yi a shekarun baya. Sarki Philippe ya gana da Shugaba Felix Tshisekedi a farfajiyar majalisar dokoki da ke birnin Kinshasa. A ranar Jumma'ar wannan makon kuma, sarkin zai yi wa wasu daliban jami'a jawabi. A karshen mako tawagar sarkin na Beljiyam za ta yada zango a wani asibitin kula da mata a birnin Bukavu, domin kwarewar da asibitin ya yi wurin tallafawa matan da aka ci zarafinsu a kasar ta Kwango.