Kyanda ta kashe dubban rayuka a Kwango
December 5, 2019Talla
Hukumar ta lafiya ta danganta karancin alluran riga kafi da kuma abinci a matsayin manyan dalilan da suka taimaka wa karuwar mace-macen a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon.
Abin kuma ya fi shafar mazauna arewacin lardin Kivu ne da ke fama da matsalar Ebola. Akwai mutane sama da miliyan biyu da ke bukatar alluran na riga kafi a yankin.
Sai dai aikin na fuskantar matsaloli a yankin saboda hare-haren da ake kaiwa kan jami'an lafiya da kuma na agaji.