Kyama ga likitocin Ebola | Labarai | DW | 20.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kyama ga likitocin Ebola

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a guji kyamatar likitocin da ke kula da masu cutar Ebola, musamman a kasashen da cutar ta fi kamari.

Majalisar ta yi kiran ne ga kasashen da ke fama da annobar cutar Ebola mai saurin kisa a yankin yammacin Afirka, inda ta ce likitocin na yin aiki tukuru domin ganin an kawo karshen cutar. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-moon ne ya yi wannan kira a yayin da ya isa kasar Guinea a rana ta biyu ta ziyarar da yake yi domin bayyana godiyarsa ga likitocin da ke kula da masu Ebolan a kasashen da cutar ta fi kamari. Kididdigar baya-bayan nan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar dai, ta nunar da cewa kawo yanzu mutane dubu 7,373 ne suka rasa rayukansu sakamakon Ebola a kasashe uku da cutar ta fi kamari a yankin yammacin Afirka. Ban Ki-moon dai ya fara ya da zango ne a Laberiya kafin daga bisani ya isa kasar Saliyo, inda a Asabar din nan ya isa kasar Guinea yayin da kuma zai kammala ziyarar ta sa a sansanin jami'an yaki da cutar Ebola na Majalisar Dinkin Duniya (UNMEER) da ke kasar Ghana bayan ya ziyarci kasar Mali.