Kwaskwarima a gwamnatin Somaliya | Siyasa | DW | 11.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwaskwarima a gwamnatin Somaliya

A wannan mako ne aka sanar da sunayen ministocin gwamnatin Somaliya, inda aka zabi mutane 25, wadanda kwararru ne amma ba 'yan siyasa ba.

'Yan majalisar dokoki dai na adawar cewa goma daga cikin mutane 25, duk tsaffin kuraye ne a gwamnatin da ta shude. Amma dai yanzu an samu fahimtar juna tsakanin Firaminista Omar Abdirasheed Ali Sharmake, inda kuma gwamnatin ke da rinjayen kujeru cikin majalisar ministocin. Andrew Atta-Asamoah masanin al'amuran kasar Somaliya ne da ke cibiyar nazarin harkokin tsaro a Peritoriya.

"In ka duba jerin sunayen akwai sabbin fiskoki, wadanda ba a sansu cikin fagen siyasar kasar ba. To amma kuma hakan yana nasaba ne da bukatar samun mutanen da a tarihi ba'a sansu da kasancewa cikin rikicin siyasar kasar Somaliya ba. Kana da yunkurin ganin a mika sunayen da jama'a za su aminci da su, wadanda ke da kudurin share wa Somaliya hawaye"

A yanzu babban aikin da ke gaban sabbin ministocin shi ne, kawo karshe rikita-rikitar siyasar da ta yi sanadiyar dai-daita Somaliya. Inda ake saran za su shirya kundin tsarin mulki da za abi, wanda kuma ake saran za a yi kuri'ar jin ra'ayin jama'a a kansa. Kana bayan haka ana fatan su iya shirya zaben kasar. Sama da shekaru 20 Somaliya na fama da yaki, inda ko a makon jiya, kungiyar Al-Shabab ta harbe wani dan majalisar dokoki, sai dai duk da haka waklin DW a Mogadishu, Mohammed Hussein ya ce duk haka an dan samu saukin lamarin:

"Yanayin tsaron ya yi sauki matuka. Domin ana samun jami'an tsaro da ke sintiri cikin dare kan tituna a daukacin biranen"

A yakin da gwamnatin Somaliya ke da yan ta'adar Al-Shabab suna samun marawar rundunar sojojin Tarayyar Afirka da kuma kasar Amirka wanda ke amfani da jirage masu sarrafa kansu, inda a makon da ya gabata faramkin da Amirka ta kai ya yi nasar hallaka wani fitaccen kwamandan kungiyar Al-Shabab mai suna Yusuf Dheeq, hakan kuwa babban koma baya ne ga 'yan bindigar. A cewar Atta-Asamoah:

"Al-Shabab ta yi asara mai yawa, kama daga yankin da suke iko da su sannan yanzu ba sa iya kai hare-haren da suke kaiwa a da. Hakan na nasaba da rasa mayakansu dama irin namjin aikin da sojojin Tarayyyar Afirka ke yi. bugu da kari da yadda gwamnatin kasar Somaliya ke kara samun karfi"

A yanzu haka dai abin da Somaliya ke fata shi ne, kasashen da ke bata tallafin kudi su kara azama ta yadda sabuwar majalisar kan iya aiki domin kuwa kasar Somaliya ta dogara ne kacokan bisa tallafin da take samu daga wajen kungiyoyi kamar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin