1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar barkewar rikici a KWango

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 11, 2019

Cocin Katolika da ke Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kasashen Faransa da Beljiyam na ci gaba da nuna shakkunsu kan sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar ta Kwango.

https://p.dw.com/p/3BLyG
DR Kongo Politiker Felix Tshisekedi
Felix Tshisekedi da hukumar zaben kasar Kwango ta ce ya lshe zaben shugaban kasa.Hoto: Getty Images/AFP/V. lefour

Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar zaben kasar CENI ta bayyana dan takara Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben. Dama dai jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben, babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar adawa Martin Fayulu ya bayyana sakamakon a matsayin wanda aka kirkira.

 
Shugabanni Cocin Katolikan na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango dai, sun nunar da cewa sakamakon wanda ya ayyana Tshisekedi a matsayin dan takarar da ya lashe zaben, ya sabawa sakamakon da masu sanya idanu 40,000 da cocin ta tura suke da shi. Wata majiya ta diplomasiyya ta nunar da cewa sakamakon da ke hannun shugabannin cocin ya nuna Fayulu a matsayin wanda ya lashe zaben, ko da yake cocin ba ta bayyana sunan kowa a matsayin wanda yai nasara ba. Rahotanni sun nunar da cewa al'ummar kasar na cikin fargabar kada a maimata tashin hankalin da ya afku bayan zabukan 2006 da 2011.