Wani Pasto ya rasa ransa sakamakon kamuwa da cutar Ebola
July 16, 2019Talla
Mutumin da ya rasu ne kwanaki bayan an gano da ya kamu da cutar. Kafin ya rasu mutumin malamin addini ne da ya sha yin wa'azi tare da yin mu'amala da jama'a da dama kafin cutar ta yi sanadiyyar mutuwarsa.
Mutuwar Paston ta haifar da fargaba ga al'ummar yankin na Goma, daya daga cikin yankunan kasar mafi yawan al'umma a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Sai dai gwamnan yankin ya bukaci jama'a da su kwantar da hankulansu tare da kasancewa a cikin tsafta.
Cutar ta Ebola ta hallaka akalla mutane 1660 sakamakon kamuwa da ita a yankunan kasar dabam-dabam.