1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Kwango

Fursunoni 129 sun mutu a kurkukun Makala a Kwango

September 3, 2024

Akalla mutane 129 suka mutu a wani yunkurin tserewa daga gidan yari mafi girma na Makala da ke a birnin Kinshasha na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/4kEAQ
Hoto: AP Photo/picture alliance

 Ministancikin gida na kasar Jacquemain Shabani a cikin sanarwa da ya fitar ya ce yawancin wadanda suka mutu sun cikka ne a cikin turmutsitsi, wanda wasu suka suke. Sai dai ya ce 24 daga cikin wadanda suka mutun 'yan sanda ne suka bindigesu har lahira, yayin da ya ce wasu matan sun fuskanci fyade sai dai bai bayar da karin bayyani ba. Gidan yarin na Makala, wanda shi ne mafi girma a yankin tsakiyya na Afirka yakan daukar mutum, dubu daya da dari biyar to amma an loda masa kusan fursuna dubu 14. Abin da kungiyoyi kare hakkin bil Adama ke yin tsokaci a kan yawan   cinkoson.