1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Kwango

Me ya sa ba a tsagaita bude wuta ba a gabashin DRC?

August 27, 2024

Fada na ci gaba da kazanta a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanya wa hannu tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen M23 cikin watan jiya.

https://p.dw.com/p/4jy0u
Hoto: Alain Uaykani/Xinhua/picture alliance

 Dakarun gwamnati da mayakan tawayen M23 na ci gaba da kai wa juna hare-hare a gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwangon ne kuwa, inda abin damuwa ma a yanzun ke zama kara matsowa da rikicin ke yi zuwa yankunan da ake da cunkososn fararen hula a cikin su. Wuraren da ake bayyana fargabar rikicin na iya cinyewa dai, su ne Lake Edward da ma arewacin Lardin Kivu, wadanda ke kusaci da kasashen Ruwanda da Yudanga.

Kongo-Krieg 2000 bis 2003 | UPDF in MPODWE Uganda
Hoto: PETER BUSOMOKE/AFP

 Wasu rahotannin da suka fito a baya-bayan nan, sun nuna cewa a ranar Lahadin da ta gabata, ‘yan tawayen M23 sun karbe iko da garin Kirumba da ke da matukar muhimmanci a yanki Karbe garin ya zo ne bayan jerin wasu da suka yi ta shiga hannun kungiyar, wasu ma ba tare da wata turjiya ba, tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi cikin watan jiya. Wani mai nazarin al'amura a lardin Kivu, Jack Kahorha, ya nuna irin ta'asar da M23 ta sake dawowa da ita a yanzun. "Babu yadda za a iya shiga garin Goma a yanzu, saboda kawanyar da ‘yan tawayen Nyiragogon ta M23 suka yi wa cibiyar ta arewacin Kivu. Kuma yadda al'amura ke tafiya a halin da ake ciki, babu wani fata na samun zaman lafiya muddin dai aka gaza tsayar da matsaya ta neman tattaunawar sulhu. Tsawon   sheakru 30 ke nan muna cikin hali na yaki. Kawai dai abu ne dai da ya ki ci ya ki cinyewa.”

DR Kongo Rethy | militante Milizgruppe URDPC/CODECO
Hoto: ALEXIS HUGUET/AFP

A shekara ta 2021 ne kungiyar tawayen ta M23 ta yi a karbe yankuna, a lokacin da ta sake dawowa da karfinta. Ana kuma tsananta zargin gwamnatin Ruwanda da goya wa kungiyar baya.Gwamnatin Kwangon na fadin Ruwanda na kara taimako ga ‘yan tawayen musamman wajen ba su bindigogi da albarusai gami da karin mayaka. Yayin da Ruwandar ke musanta hakan a gefe guda, cikin watan Fabrairu ta yarda cewa sojojinta da ma wasu makamai na gabashin Kwangon, amma  kan abin da ta nuna matakin kare kanta ne saboda yawan sojojin Kwangon da ke a can. Cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar DW, shugaban kasar Malawi   Lazarus Chakwera, wanda shi ne ke jagorantar kungiyar kasashen gabashin Afirka, ya ce babu abin da zai fi a zauna lafiya a yankin.

DR Kongo | Armee auf Patrouille in Goma, Provinz Nord-Kivu
Hoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

"Ci gaba dai ba ya samuwa sai da zaman lafiya. Ko da ana ganin wasu na fakewa da guzuma suna harbin karsana, ko kuma su wa ke da iko a kan albarkatu da makamantansu, za dai mu tabbatar da daukar mataki na ganin an kare talakawa wadanda su ne masu rauni cikin al‘umma." Yayin dai da sojojin kungiyar SADC ta yankin gabashin Afirka ke kokarin ganin sun maganta hannayen Ruwanda a rikicin karkashin bukatar gwamnatin Kwango da ke mamba a kungiyar, ana kallon yiwuwar rincabewar lamura musamman a yankin wanda ke da nasaba da siyasar iyaka. Kafin yanzun dai sojojin Ruwanda da na kungiyar ta SADC na aiki ne tare bisa kudurin ganin bayan mayaka masu da'awar kafa daular Islama a arewacin kasar   Mozambik.