Kwalera ka iya zama gagarabadau a Haiti | Labarai | DW | 23.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwalera ka iya zama gagarabadau a Haiti

An tabbatar da mutuwar mutane 200 a Haiti sakamakon cutar Kwalera

default

Mutane masu fama da cutar Kwalera suna karɓar magani a wani asibiti dake Saint Marc, Haiti

Ma'aikatan kiwon lafiya na aiki tuƙuru don shawo kan annobar cutar Kwalera da ta halaka fiye da mutane 200 a ƙasar Haiti, wadda ke gwagwarmayar sake gina kanta biyo bayan wata mummnar girgizar ƙasa a cikin watan Janeru da ta yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 250. Ƙungiyoyin taimakon jin ƙai sun kasance cikin shirin ko-takwana domin daƙile yaɗuwar cutar zuwa babban birnin ƙasar wato Port-au-Prince, inda mutane sama da miliyan ɗaya suka yi cincirindo a sansanoni. Dr. John Arbus mataimakin daraktan ƙungiyar kiwon lafiya ta Pan America ya ce yana fargaba halin da ake ciki zai ƙara yin muni.

"Bisa la'akari da masaniyarmu akan yaɗuwar annobar kwalera a baya, bisa ga dukkan alamu wannan cutar za ta bazu zuwa yankuna da dama, musamman a tsakanin jama'a da ba su da wata cikakkiyar kariya kasancewa sun daɗe ba su yi fama da cutar Kwalera ba."

Kawo yanzu mutane sama da 3000 ake yiwa jiyyar ƙwayoyin cutar a faɗin ƙasar baki ɗaya. Tun wasu watanni da suka gabata ƙungiyoyin agaji ke yi ta kashedin cewa rashin wurare masu tsabta da rashin tsabtataccen ruwan sha ka iya haddasa yaɗuwa cututtuka.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala