1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalara ta kashe mutane a Nijar

October 3, 2018

Mutane da dama sun salwanta a Nijar sakamakon ibtila'in cutar kwalara a wasu sassa na kasar.

https://p.dw.com/p/35vEJ
Cholera in Simbabwe
Hoto: AP

Ma'aikatar lafiya a Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar mutum 68 sakamakon kamuwar da suka yi cutar amai da gudawa wato kwalara, wadda ta faro cikin watan Yulin da ya gabata.

A cewar ma'aikatar a wannan makon kadai, an sami sama da mutum dubu 3,600 da cutar ta kama.

Matsalar ta samu asali ne sakamakon gurbatar abinci da kuma ruwan sha da kwayoyin kwalarar, da kuma ke kisa cikin gaggawa, muddin aka gaza samun dauki na likita.

Cutar dai ta yadu ne a tsakiyar jihar Maradi da arewacin Tahoua da gabashin Zinder gami da kudu maso yammacin Dosso.

Asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya da ma hukumar lafiya ta duniyar, duk sun ce kashi 37 cikin dari na al'umar Maradi ne ke samun ruwan sha da kuma muhalli masu tsafta.