1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalara na barna a Mozambik

March 29, 2019

Cutar kwalara na ci gaba da zama wani hadari a Mozambik daya daga cikin kasashen da suka fuskanci bala'in guguwa da ambaliya a kudancin Afirka

https://p.dw.com/p/3FtBF
Mosambik Cholera Idai Zyklon
Hoto: Getty Images/Y. Chiba

Bayanan da ke fitowa daga kasar Mozambik, na cewa alkaluman wadanda suka kamu da cutar kwalara a yankin Beira a yanzu sun karu daga mutum biyar zuwa 138.

Sabbin alkaluman dai na zuwa ne, yayin da hukumomi da kungiyoyin agaji ke fadi tashin dakile yaduwar cutar a yankin da ibtila'in mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ta fi yi wa lahani.

A ranar 14 ga watan nan na Maris ne dai Ibtila'in ya shiga Mozambik da Malawi da kuma Zimbabuwe, inda akalla hukumomi suka ce mutum 700 sun salwanta.

Akwai kuma fargabar da kungiyoyi ke yi na cewar dubban ne mutuwar ta shafa kai tsaye a kasashen na kudancin nahiyar Afirka.

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumomi a Mozambik din suka soma bayyana matsalar ta Kwalara a yankin na Beira da ya fuskanci ambaliyar ruwa.