Kutsen yanar gizo ya kawo tsaiko a Turai | Labarai | DW | 27.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kutsen yanar gizo ya kawo tsaiko a Turai

Masu satar kutse ta internet sun haddasa gagarumin tsaiko a hada hadar yanar gizo a kasashen Turai inda lamarin ya fi yin muni a kasar Ukraine.

Kamfanoni da jami'an gwamnati sun ruwaito katsewar al'amura a babbar tashar samar da wutar lantarki ta Ukraine da bankuna da kuma ofisoshin gwamnati.

Kamfanin makamashi na Rosneft na Rasha shi ma ya sanar da cewa yana daga cikin wadanda aka yiwa kutse da kuma kamfanin AP Moller Maersk da yace lamarin ya shafi dukannin rassan sa na harkokin kasuwanci.

Mukaddashin Firaministan Ukraine din Pavlo Rozenko ya wallafa wani bakin hoto na kwamfuta a shafinsa na Twitter yana cewa na'urorin kwamfuta a fadar gwamnati sun tsaya cik.

Musamman kutsen ya shafi kamfanoni a kasashen Britaniya da Rasha da kuma Ukraine.