Kusan mutane 40 sun halaka a rikicin kasar Yemen | Labarai | DW | 21.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kusan mutane 40 sun halaka a rikicin kasar Yemen

Mayakan Houthi na kasar Yemen sun yi tsinke wa fadar shugaban kasar Abd-Rabbu Mansour Hadi

Mutane 35 sun halaka wasu kusan 100 suka samu raunika sakamakon musayen wuta tsakanin sojojin kasar Yemen da tsagerun 'yan shia na kungiyar Houthi. Majiyoyi asibiti da na tsaro sun ce lamarin ya faru a babban birnin kasar na Sanaa.

Mayakan Houthi na kasar Yemen sun yi tsinke wa fadar shugaban kasar Abd-Rabbu Mansour Hadi a wannan Laraba, amma sun ce ba su da niyar kifar da gwamnati, duk da suna iko da babban birnin kasar na Sanaa.

Kungiyar ta Houthi ta Shia wadda take dasawa da Iran ta kasance mai karfi a kasar ta Yemen da ke da mutane milyan 25 galibi suna zama cikin matsanancin talauci. Kwamitin sulhu na MDD ya yi tir da harin da aka kai fadar Shugaban kasar ta Yemen Abdrabuh Mansur Hadi.