Kuri′ar amincewa da yarjejeniyar Brexit | Labarai | DW | 19.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kuri'ar amincewa da yarjejeniyar Brexit

Al'umma na shirin yin tattaki a birnin Landan a yayin da 'yan majalisa ke shirin kada kuri'ar amincewa da yarjejeniyar Firaiminista Boris Johnson kan ficewar Britaniyya daga Kungiyar EU.

'Yan majalisar dai za su kada kuri'an bisa nuna amincewa ko akasin hakan da daftarin na mista Johnson. Firaiministan da ya dage kan ficewar kasar koda ba da yarjejeniya ba, yana neman goyon bayan 'yan majalisar a matakin da zai bai wa Britaniyyan damar raba gari da kungiyar ba tare da an fuskanci tarnaki ba. A ranar talatin da daya ga wannan watan na Oktoba, wa'adin ficewar ke cika.