1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kurdawan Iraki na neman 'yancin kai

July 4, 2014

Kurdawan Iraki na cigaba da fafutukar ballewa daga kasar da ke fama da hare haren masu tayar da kayar baya da kuma neman kafa kasar musulunci.

https://p.dw.com/p/1CVXg
Irak Iran Kurden PJAK Kämpfer für Kurdistan
Hoto: Safin Hamed/AFP/Getty Images

Yayin da 'yan tawayen kungiyar nan ta 'yan Sunni ta ISIS ke cigaba da mamaye yankunan kasar Iraki, shugaban yankin Kurdawa na kasar ya nemi 'yan majalisar yankin da su mika bukata ta yin kuri'ar raba gadama don samun cikakken 'yancin cin gashin kai.

Shugaban na Kurdawan Massoud Barzani ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da 'yan majalisar inda ya bukace da su gaggauta kafa hukumar da zabe da za ta gudanar da wannan aikin don kaiwa ga cimma bukatarsu ta ballewa.

Mr. Barzani ya ce lokaci ya yi da Kurdawa za su zabawa kansu makoma maimako su jira wasu mutane na daban su yi musu hakan kasancewar yanzu haka kasar na cikin wani yanayi na rudani.

Kurdawan na Iraki kimanin miliyan biyar sun jima suna rajin ballewa daga Iraki, lamarin da ake kallo a matsayin wata babbar baraza ta cigaba da dorewar Irakin a matsayin tsintsiya madauiki daya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar