Kungiyoyn kare yancin dan Adam sun soki Kenya | Labarai | DW | 09.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyoyn kare yancin dan Adam sun soki Kenya

Kenyan ta kaddamar da samamai kan wadanda take tuhuma da aikata ta'addanci a kasar, inda ta tsare dubban jama'a abinda kuma ya sa ake sukar lamarin

A kasar Kenya kimanin mutane 3000 aka kama wadanda duk musulmai ne da gwamnati ke tuhuma da hannu, bisa ayyukan ta'addanci da ke karuwa a kasar. Kakakin 'yan sanda Masaoud Mwinyi ya ce bayan tankade da aka yi, an sallami wasu mutanen, amma har yanzu ana tsare da kimanin mutane 450, karkashin dokar yaki da ta'addanci, wanda ta bai wa 'yan sanda damar tsare mutum sama da sa'o'i 24. Kimanin jami'an tsaro dubu shida suka shiga samamen da aka kaddamar a biranen Nairobi da Mombasa. Kungiyoyin kare 'yancin dan adam sun soki kamen da 'yan sandan suka yi, inda suka ce dukkan wadanda aka kama 'yan asalin kasar Somaliya ne. Kenya dai ta yi fama da ayyukan ta'addanci, wanda take dora wa kungiyar al-Shabab laifi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasiru Awal

AP