1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta fara ficewa daga Afganistan

Binta Aliyu Zurmi
April 29, 2021

Rundunar kungiyar tsaro ta NATO ta fara aikin kwashe dakarunta daga kasar Afganistan a cewar sanarwar da shugabannin kawance suka ba wa kamfanin dillancin Labaru na Faransa AFP a yau Alhamis.

https://p.dw.com/p/3slfl
Afghanistan Kabul Anschlag Botschaftsviertel
Hoto: Reuters

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da shugaban Amirka Joe Biden ya sanar da aniyarsa ta janye dakarun kasarsa daga kasar Afganistan kuma ya yi nasarar shawo kan sauran kasashen da ke taimakawa a yakin da ake yi da 'yan Taliban da su ma su fice.

Sanarwar ta kara da cewar duk wani yunkuri na hari daga mayakan na Taliban a wannan lokacin zai gami da fushin kungiyar. Ana sa ran kammala janye dakaru a cikin 'yan watanni masu zuwa nan gaba.

A yayin da su kuma Amirka za su fara na su a watan Satumbar shekarar nan, watan da kasar ke cika shekaru 20 da kaddamar da yaki a Afganistan tun bayan harin 11 ga watan Satumban 2001 da ake wa lakabi da 9/11, da ya hallaka daruruwan mutane a Amirka.