Kungiyar Taliban ta sako mutane 235 | Labarai | DW | 08.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Taliban ta sako mutane 235

Kungiyar Taliban a Afganistan ta sako wasu mutane 235 da ta yi garkuwa da su a wani kauye mai suna Mirzawalang.

Kungiyar Taliban a Afganistan ta sako wasu mutane 235 da ta yi garkuwa da su a wani kauye mai suna Mirzawalang da ke yankin arewacin kasar. Mayakan na Taliban sun yi garkuwa da wadanan mutanen ne a  wani farmaki da suka kai kauyen a can baya inda suka hallaka fararren hula fiye da hamsin.

Akwai mata da kananan yara a cikin wadanda aka sakon. Kakakin gwamnan yankin Zabihullah Amani ya ce an cimma matsaya da sa bakin dattijan kauyen da ma bangaren wakilan yankin, ya kuma kara da cewa akwai wasu da ba za a iya tantance yawansu ba da mayakan ke ci gaba da yin garkuwa da su.