Kungiyar NATO za ta kara kaimi a Afghanistan | Labarai | DW | 09.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar NATO za ta kara kaimi a Afghanistan

Kungiyar tsaro ta NATO ta yanke shawarar bada karin tallafi ga kasar Afghanistan sakamakon halin da take ciki na tabarbarewar al'amuran tsaro.

Shugabannin kasashe guda 28 na kungiyar tsaro ta NATO da ke yin taro a birnin Warsaw na kasar Poland a kwanaki na biyu jere sun tattara kudade kusan biliyan daya na dala, domin taimaka wa Amirka a cikin shekaru uku masu zuwa a game da shirinta na tsara rundunar sojojin Afghanistan. Jens Stoltenberg shi ne babban sakataren kungiyar tsaron ta NATO da ya yi karin haske.

Ya ce: ''Da farko mun amince mu cigaba da kawo wa rundanar kawance ta dakarun da ke a Afghanistan dauki har bayan wannan shekara da muke ciki har zuwa shekara ta 2020.''

A badi dai ana sa ran dakarun kasashen kawance hade da Amirka a Afghanistan din za su kai har dubu goma sha biyu.