Kungiyar EU: Bukatar bude iyakoki domin masu yawon bude ido | Labarai | DW | 13.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU: Bukatar bude iyakoki domin masu yawon bude ido

Kungiyar EU ta fara shirin bude iyakoki da janye dokar hana shige da fice tsakanin kasashen kungiyar duk da fargabar farfado da harkokin yawon bude ido a wannan lokaci na annobar corona.

Kungiyoyin kamfanonin da suke shirya yawon bude ido sun yabawa wannan aniya da suka bayyana da matakin farko na farfado da ayyukan yi, koda yake a nata bangaren hukumar kungiyar ta EU ta nunar da cewar wannan bukata ba tilas ba ce kan dukkan kasashe 27 mambobin kungiyar.

Shirin daukar wannan mataki na zirga-zirga tsakanin kasashen kungiyar EU ya zo ne bayan wasu daga cikin kasashen da suka yi fama da annobar ta corona sun bayyana shakku game da janye dokar shige da fice tsakaninsu da sauran kasashe.

Daga cikin sharuddan da kungiyar ta shirya domin zirga-zirga tsakanin kasashen, akwai umartar kamfanoni da filayen jiragen sama su tilasta wa fasinjoji sanya takunkumi da kuma sake tsarin tantancewa da na daukar kaya domin kaucewa cunkoson fasinjoji.