Kungiyar ci-gaban mata manoma a Kano | Himma dai Matasa | DW | 05.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kungiyar ci-gaban mata manoma a Kano

Mata na hobbasa wajen ganin cewar ana damawa da su a fannoni na rayuwa ciki har da noma, tare da tallafin wasu kungiyoyi

Manoma mata na yankunan karkarar wasu jihohin arewacin Najeriya sun fara samun ci gaban tattalin arziki da na jin dadin rayuwa albarkacin tallafi da shawarwarin wata kungiyar kyautata rayuwarsu da ake kira WOFAN da ke Kano.

Hajiya Salamatu Garba ce ta kafa kungiyar, da ke kokarin ganin cewar an cire mata daga kangin talauci da suke fama da ita sakamakon rashin aikin yi.

Kungiyar na bada muhimmanci kan abubuwa da suka hadar da shi kansa noman da samar da kayayyakin aiki kamar feshi da taki, sai samar da ruwan sha mai tsafta da kuma kula da muhalli.

Sauti da bidiyo akan labarin