Kuncin rayuwa na addabar mazauna Aleppo | Siyasa | DW | 12.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kuncin rayuwa na addabar mazauna Aleppo

Mako na biyu ke nan ake ci gaba da gumurzu na samun madafan ikon Aleppo, batu da ya jagoranci zanga-zangar adawa dangane da halin kunci na mazauna yankin.

Mazauna unguwar Sakhur da ke kudancin Aleppo sun yi Allah wadai da hare-haren da jiragen Rasha da Siriya suka ci gaba da kaiwa sassan da ke karkashin ikon 'yan tawaye, duk da sanarwar da Rasha ta yi,na fara aiki da kwarya-kwaryar tsagaita wuta na tsawon sao'i uku a kullum, don ba da damar shigar da kayayyakin agaji.

Suma mazauna kudancin kasar da ke karkashin dakarun gwamnati, yadda rokokin da 'yan tawaye suka harba, gwamnati ta ce sun halaka fararen hula hudu. Mazauna yankunan da suma sukai zanga-zangar kira da a aiwatar da tsagaita wutar ka'in da na'in sun koka kan irin matsanancin halin da suka tsinci kansu cikinsa:

"Dakarun sojin da ke garkuwa damu sun ce mana, idan muka kuskura muka fita zasu harbe mu. Mako guda ke nan muna kudundune cikin gida, muna jin rokoki na ta fadawa kan makwabtanmu. Allah dai ya sa muna da sauran shan ruwa a duniya,s hi yasa da misalin karfe ukun dare, muka silale muka fice daga yankin."

Likitoci 15 daga cikin daruruwan da suka rage a birnin na Aleppo, wadanda suka ce basu barin garin sai dai gawarsu. Sun rubuta wata doguwar wasika ga Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen da ke cewa, su kawayen al'ummar Siriya ne. Tana bayyana musu irin alhakin da ya rataya a wuyansu dangane da matsanancin halin da al'ummar ke ci, yadda suka kebe kasar Amirka wajen caccaka, kan ko oho da shugabanta Obama ya ke nunawa kan batun Siriya.

Sauti da bidiyo akan labarin