Kudancin kasar Sudan na ci gaba da fuskantar Hare-hare | Labarai | DW | 23.04.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kudancin kasar Sudan na ci gaba da fuskantar Hare-hare

Wani rahoto da cibiyar bincike kan yara kanana da rikici dake kasar Amirka ya fitar ya bayyana cewar akalla asibitoci hamsi aka kaiwa hari a kudancin kasar Sudan daga shekara ta 2016 zuwa 2017.

Südsudan UN denken über Verstärkung von Unmiss nach (Reuters/A. Ohanesian)

Al'ummar kudancin kasar Sudan

Rahoton ya kara da cewar cikin hare-hare 750 da 'yan tawaye su ka kai a cikin kankanin lokaci, kayan agaji sun gaza kaiwa ga masu bukata sakamakon hana shige da fice yankunan da ke fama da rikicin da 'yan tawayen suka yi a kasar ta Cibiyar ta zargi bangaren gwamnatin da kuma na 'yan tawayen da konewa tare da sata da mamaye asibitoci da kuma tsare likitoci da ma'aikatan ayyukan agaji a matsayin dabarun yaki.