Kotun tsarin mulkin Burundi za ta duba yunkurin tazarce na shugaba Nkurunziza | Labarai | DW | 29.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun tsarin mulkin Burundi za ta duba yunkurin tazarce na shugaba Nkurunziza

Da ma dai 'yan adawa sun ce yunkurin ya saba wa dokar kasa da kuma yarjejeniyar zaman lafiyar shekarar 2006, da ta kawo karshen yakin kasar.

Kotun kare kundin tsarin mulkin kasar Burundi za ta duba halalcin yunkurin shugaban kasa Piere Nkurunziza na neman wa'adin mulki karo na uku. Majalisar dattawan kasar ta ba da wannan sanarwa a wannan Laraba bayan kwashe tsawon kwanaki ana zanga-zangar adawa da aniyar shugaban na neman tsayawa takara a zaben da zai gudana cikin watan Yuni. Yanzu haka an mika wa kotun wata takardar neman ta yi bayani bisa halalcin wannan yunkurin karkashin tsarin mulkin kasar, matakin da 'yan adawa suka ce ya saba wa dokar kasa da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2006 wadda ta kawo karshen yakin kasar.