Kotun The Hague ta sake tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 50 wa Taylor | Siyasa | DW | 26.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kotun The Hague ta sake tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 50 wa Taylor

A Freetown na ƙasar Saliyo, jama'a sun yi ta nuna farin ciki dangane da wannan hukunci da kotu ta ɗaukaka, sai dai ƙasashen Afirka da dama sun fara adawa da wannan kotun

Former Liberian President Charles Taylor appears in court at the Special Court for Sierra Leone in Leidschendam, western Netherlands, January 22, 2013. Taylor, who was sentenced to 50 years in prison by the Hague in May 2012, appealed against his conviction for supporting Revolutionary United Front rebels during Sierra Leone's 11-year civil war. REUTERS/Peter Dejong/Pool (NETHERLANDS - Tags: POLITICS CONFLICT CRIME LAW)

Charles Taylor

Charles Taylor tsohon shugaban ƙasar Liberiya ya sami hukuncin ɗauri a gidan yari na tsawon shekaru 50. Kotun ɗaukaka ƙara ta musamman wa ƙasar Saliyo dake The Hague ta yanke wannan hukuncin yau, bayan da a bara aka sami Mr Taylor da laifuka 11 waɗanda suka haɗa da fyaɗe, da kisar gilla da kuma amfani da ƙananan yara a matsayin sojoji. Wannan hukunci ya zauna ne bayan da Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da shi bayan ta gudanar da nata binciken.

Mai sharia George Gelaga King ke nan yake gabatar da hukuncinsa dangane da ƙarar da tsohon shugaba Charles Taylor ya ɗaukaka

Charles Taylor zai ci gaba da kasancewa a hannun kotu na musamman na Saliyo kafin a kammala shirye-shiryen mayar da shi inda zai fuskanci wannan hukunci

A yayin da Charles Taylor zai ci gaba da kasancewa a hannun kotun ya kuma fuskanci hukuncin ɗauri na shekaru 50 mai shigar da ƙara Brenda Hollis na taka tsantsan wajen kwatanta hukuncin a matsayin nasara

"Ba daidai ba ne a ce yau rana ce ta murna ko yin buki, yanayin laifukan da aka tabka ba zasu bari a yi murna ba, amma kuma rana ce ta yin waiwaye kan laifukan da aka tabka da kuma hukuncin da aka yanke, da irin juriyar da waɗanda abin ya shafa suka nuna da ma al'ummomin ƙasar Saliyo"

Matsayin masu shigar da ƙara

Brenda Hollis ta kuma yi wa mutane tunin muhimmancin wannan shari'a da ma hukuncin da aka yanke

Sashen ɗaukaka ƙara yau ya tabbatar da abin da shari'ar farko ya fayyace, cewa shugabanin ƙasashe zasu ɗauki alhakin duk wani laifin yaƙi da sauran laifukan ƙasa da ƙasa da suka tafka, kuma babu wanda ya fi ƙarfin doka, hukuncin yau ya nuna cewa a shugabanci ba ƙarfin iko kaɗɗai mutun zai nuna ba, amma dole ya ɗauki ɗawainiyar duk wasu abubuwan da za su biyo baya

Makomar Charles Taylor

Lauyan Charles Taylor Morris Anyah ya ce wannan shari'a zai yi tasiri kan shari'ar ƙasa da ƙasa, ya yi fatan cewa kotun ɗaukaka ƙarar za ta bi tafarkin hukuncin da aka yanke a kotun hukunta manyan laifukan yaƙi ta Yugoslaviya inda kotun ta wanke wani tsohon jami'in Serbiya daga zarge-zargen da ake yi masa na taimakawa wajen haddasa rigingimu, bayan da ta yanke hukuncin cewa akwai waɗansu mahimman abubuwan da take buƙata kafin ta kai ga yanke irin wannan hukunci

*** ARCHIVFOTO*** FILE - In this May 20, 2010 file photo, British model Naomi Campbell arrives for the amfAR Cinema Against AIDS benefit, during the 63rd Cannes international film festival, in Cap d'Antibes, France. Judges at the Special Court for Sierra Leone have rejected Wednesday Aug. 4, 2010 a final protest from Charles Taylor, clearing the way for model Naomi Campbell to testify at his war crimes trial. Taylor's lawyer had objected to Campbell testifying, arguing that the prosecution had not provided a summary of her likely testimony.(AP Photo/Matt Sayles, File)

Naomi Campbell daya daga cikin wadanda suka ba da shaida

A sakamakon wannan shari'ar dai za a iya cewa an sami sauyi a yanayin yanke hukunci a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, domin taimakawa wajen haddasa rigingimu na nufin abubuwa daban-daban a kowace kotun da ke The Hague, domin idan da Charles Taylor ya gurfana a gaban kotun da ke hukunta manyan laifukan Yugislaviya ne da wata ƙila an sami sakamako daban, kuma wannan kotun bai fi tazarar kilometa 10 tsakaninta da wannan kotun ba

Duk da cewa lauyan Charles Taylor na takaicin wannan hukuncin ya duƙufa wajen ganin yadda zai tabbatar ya cigaba da ganin 'yan uwa da abokan arziƙinsa.

Martanin 'yan Saliyo dangane da wannan shari'ar

Ga wasu daga cikin ra'ayoyin 'yan Saliyo bayan da aka yanke wannan hukunci

"A tunani na dole ne a sake duba wannan shari'ar, kuma dole mu fahimci abin da ake nufi domin an cika zuwa Afirka a ɗauki shugabaninsu a gurfanar da su ba tare da an gudanar da bincike mai zurfi ba a kuma kira shi adalci"

Wannan kuwa cewa yake yi, ina farin ciki, a gani na an kamanta adalci, kuma wannan zai zama darasai ga sauran shugabanni, domin su san irin matakan da zasu riƙa ɗauka lokacin rikici.

A yanzu haka dai matakin samun kotunan hukunta manyan laifukan yaƙi na ƙasa da ƙasa na fiskantar suka a ƙasashen Afirka, inda shuwagabanin ke ganin kaman su kaɗai ake hukuntawa, kuma yawancinsu na yunƙurin ficcewa daga yarjejeniyar da ta samar da irin waɗannan kotuna.

Mawallafiya: Cintia Taylor/ Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin