1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Isra'ila ta dage haramcin kungiyoyin agaji a Gaza

Abdul-raheem Hassan
February 27, 2026

Kotun koli a Isra'ila ta dakatar da matakin gwamnatin Benjamin NNetanyahu, na haramtawa kungiyoyin kasashen waje guda 37 gudanar ayyukan agaji a zirin Gaza har sai kotu ta yanke hukuncin karshe.

https://p.dw.com/p/59YOs
'Yan gudun hijira da kayan agaji a Jabalia
'Yan gudun hijira da kayan agaji a JabaliaHoto: BASHAR TALEB/AFP

A karshen shekarar 2025 ne Isra'ila ta dakatar ayyukan kungiyoyin agajin saboda karewar rejistar su, kungiyoyin da matakin ya shafa sun hada da Doctors Without Borders wato likitocin na gari na kowa da kungiyar Oxfam da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Norway da kuma kungiyar CARE.

Gwamnatin Isra'ila ta kafa wa kungiyoyin sharadin gabatar da sunayen Falasdinawa da ke musu aiki kafin a sabunta rejistar kungiyoyinsu don cigaba da ayyukan agaji. Dakatar da ayyukan kungiyoyin ya jefa rayuwar fararen hula da dama a cikin hatsari sakamakon rashin magunguna da abinci.