Kotun ICC za ta yi wa Blé Goudé shari′a | Labarai | DW | 11.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC za ta yi wa Blé Goudé shari'a

Kotun kasa da kasa da ke birnin La Haye na kasar Holland, ta ce zata yi wa Charles Blé Goudé na hannun daman Laurent Gbagbo shari'a

Kotun tantance laifukan ce dai ta aminta da wadannan laifuka guda hudu da tun farko ake tuhumar sa da su, inda a halin yanzu ta mika wannan shari'a ga kotun da ke a matakin farko na shari'a a cewar wata sanarwar kotun a yau Alhamis. Sai dai kawo yanzu dai ba'a tsaida lokacin yi masa shari'ar ba, sannan kuma lawyoyin da ke kare wanda ake zargin na da hurumin daukaka kara kan wannan sakamako na aminta da laifukan da ake zargin sa da su. Shi dai Charles Blé Goudé ya taka rawar gani lokacin da ya ke jagorancin matasan kasar ta Cote d'ivoir masu goyon bayan tsofon shugaban kasar Laurent Gbagbo da a halin yanzu shima yake a gaban wannan kotu domin fuskantar shari'a.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba