Kotun ICC za ta binciken cin zarafin dan Adam a Burundi | Labarai | DW | 09.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC za ta binciken cin zarafin dan Adam a Burundi

Kotun hukuntan manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC ta ba da izinin aiwatar da bincike kan zargin cin zarafin dan Adam a Burundi daga ranar 26 ga watan Aprilun 2015 zuwa ta 26 ga watan Oktoban 2017. 

Kotun ta ICC ta sanar da wannan mataki nata ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alhamis inda ta ce binciken zai shafi laifukan da suka hada da na kisa da azabtarwa da fyade da dai sauran laifukan cin zarafin dan Adam da aka aikata a cikin kasar ta Burundi ko kuma wadanda 'yan asalin kasar suka aikata a wasu kasashen ketare. 

Wasu alkalumma da kotun ta ICC ta wallafa sun nunar da cewa mutane akalla dubu da 200 suka halaka a yayin da wasu sama da dubu 400 suka shiga gudun hijira a cikin rikicin siyasar da ya barke a kasar ta Burundi a sakamakon tazarcen Shugaba Nkurunziza. A watan Oktoban da ya gabata ne dai kasar Burundi ta kasance kasa ta farko da ta fice daga kotun ta ICC a hakumance.