Kotun ICC ta tabbatar laifi akan Ntaganda | Labarai | DW | 08.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC ta tabbatar laifi akan Ntaganda

Alkalan kotun ICC sun tabbatar da laifukan yaki da cin zarafin bil Adama akan Bosco Ntaganda, laifukan da ya aikata a lokacin rikicin Kwango mai arzikin mai.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC da ke birnin Hague ta sami fitaccen sojan yaki Bosco Ntaganda wanda ake yiwa lakabi da Terminator da laifi a shari'ar laifukan yaki da ake yi masa.

Kotun ta sami Ntaganda da laifukan yaki 13 da kuma wasu laifuka biyar da suka hada da kisan kai da fyade tare da cin zarafin al'umma a lokacin rikicin kasar Kwango tsakanin shekarun 2002-2003. Sai dai Ntaganda ya musanta tuhumar.