Kotun ICC ta sami Katanga da laifin kissa | Labarai | DW | 07.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC ta sami Katanga da laifin kissa

Madugun 'yan tawayen Kwango wanda mahukuntan Kinshasa suka miƙa shi ga Kotun a shekarar 2007, zai fiskanci hukunci saboda harin da ya hallaka fararen hula 60

Niederlande Urteil Germain Katanga Internationaler Strafgerichtshof Den Haag Verteidiger

Germain Katanga "Simba"

Kotun hukunta manyan laifuka na ICC ya sami tsohon shugaban 'yan tawayen Kwango, Germain Katanga da hannu a cikin laifukan yaƙin da aka zarge shi da su.

Katanga wanda a baya ya kasance ɗalibi mai hazaƙa, ya juya ya zama sojan da aka riƙa tsoro aka kuma riƙawa laƙabi da Simba wanda ke nufin zaƙi a harshen Swahili.

Masu shari'a a kotun dai, sun sami Katanga da laifin kissa da kwasar ganima amma kuma sun wanke shi daga zargin fyaɗe da bautar da mata dan cin zarafinsu ta hanyar jima'i, da kuma sa ƙananan yara aikin soji lokacin da ya kai hari wani ƙauye mai suna Bogoro dake yankin gabashin Kwangon.

Aƙalla fararen hula 60 suka hallaka a wannan harin wanda sojoji yara ne suka kai. Katanga ya kasance jagoran ƙungiyar tawayen FRPI kafin ya kasance Janar a dakarun sojin shugaba Joseph Kabila a shekarar 2005 kafin mahukuntan Kinshasa suka miƙa shi ga Kotun na ICC a shekarar 2007 inda aka fara masa shari'a a shekarar 2009.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Muhammad Awal Nasiru