Kotun ICC na fuskantar kalubalen kauracewa | Labarai | DW | 17.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC na fuskantar kalubalen kauracewa

Alamu na nuna kotun shari'ar manyan laifuka ta kasa da kasa ICC na cikin tsaka wuya bayan da wasu kasashe mambobinta suka baiyana aniyar ficewa daga wakilici a cikinta

Kotun duniya da ke Hague na fuskantar kalubale mafi girma tun bayan kafuwarta inda wasu kasashe mambobinta suka bayyana kuirinsu na ficewa daga wakilci a cikinta. Ta baya bayan nan ita ce Rasha inda shugaba Vladimir Putin ya rattaba hannu a kan wata takardar umarni na ficewar kasar daga ICC. Amirka ta baiyana matukar damuwa dangane da janyewar Rasha daga kotun mai shari'ar manyan laifuka. ta duniya shekaru.Kasar Shugaban kasar Philippines  Rodrigo Duterte shi ma ya sanar da cewa kasarsa za ta bi sahun Rasha don ficewa daga ICC.  Shekaru 14 da suka wuce ne dai ita ma Amirkar ta dauki makamancin wannan mataki. Kotun ta duniya dai ta fada halin tsaka mai wuya ne bayan da wasu kasashe na Afirka suka baiyana aniyar ficewa daga wakilici a cikinta. A ranar Litinin kasar Gambiya ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya cewa za ta bi sahun kasashen Afirka ta Kudu da Burundi wajen ficewa daga wakilici a kotun. Wasu kasashen Afirka da su ma suka nuna aniyar ficewa daga kotun sun hada da Kenya da Namibiya da kuma Uganda. Kasashen Afirka dai na zargin kotun da rashin yi musu adalci. Sai dai a wani abu da ke zama ba zata a ranar talata babbar mai binciken laifuka a kotu Fatou Bensouda ta sanar da cewa za ta kaddamar da bincike kan zargin sojojin Amirka da hukumar leken asiri ta Anmirka CIA sun yi zarafin mutanen da suka kama a yaki da ayyukan ta'addanci.