Kotun duniya ta daure jagoran yakin Kwango | Labarai | DW | 30.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun duniya ta daure jagoran yakin Kwango

Bayan bukatar daukaka kara bayan hukunicn da aka yanke masa a 2019, murna ta sake komawa ciki ga madugun yakin kasar Kwango, Bosco Ntaganda.

Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka a duniya da ke birnin a Hague ICC, ta tabbatar da hukuncin shekaru 30 da aka yanke wa jagoran yakin kasar Kwango, Bosco Ntaganda.

Cikin watan Yulin 2019 ne dai aka yanke wa Mr. Ntaganda hukuncin a matsayinsa na jagoran tawayen Kwangon a rikicin kasar.

An dai same shi ne da laifukan kisa da yi wa mata fyade da ma maida wasu matan bayi a lokacin yakin Kwangon a tsakanin shekarar 2002 da kuma 2003.

Alkalan kotun su 15, sun yi watsi da hujjoji 15 da Bosco Ntaganda ya gabatar inda yake kalubalantar hukuncin daurin shekaru 30 din aka taba yanke masa.

Gwiwowin Ntaganda dai sun yi matukar sanyi a lokacin da babban alkalin kotun ke karanta matsayin doka a kansa.