1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suu Kyi za ta yi zaman gidan yari

Abdourahamane Hassane
December 30, 2022

Wata kotun soji a Myanmar ta yanke wa tsohuwar firaminista Aung San Suu Kyi hukuncin daurin shekaru bakwai na zaman gidan yari.

https://p.dw.com/p/4La29
Aung San Suu Kyi
Hoto: Ann Wang/REUTERS

Kotun ta sameta da laifuka guda biyar na cin hanci da karbar rashawa. Hukuncin da aka yanke wa tsohuwar firaministan mai shekaru 77, ya kai jimillar shekaru 33 na zaman gidan yari. Sojoji sun hambarar da zababbiyar gwamnatin Suu Kyi a shekara ta 2021.Masu fafutukar kare hakkin bil' Adama sun hakikance cewa shari'ar da ake yi wa matar da ta taba lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel na da nasaba da siyasa.