Kotu ta tsawaita daure Aung San Suu Kyi | Labarai | DW | 10.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta tsawaita daure Aung San Suu Kyi

Wata kotun sojoji a Myanmar ta yanke wa hambararriyar Shugabar kasar Aung San Suu Kyi hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari, bayan samunta da karin laifuka har da mallakar rediyon "walkie-talkie" marar lasisi.

An yanke wa tsohuwar shugabar mai shekaru 76 hukuncin daurin shekaru biyu saboda karya dokar shigowa da kaya da kuma mallakar wayoyin tafi da gidanka, sai kuma karin shekara guda na samun sigina.

Gabannin wannan hukuncin, Aung San Suu Kyi na fuskantar tuhuma kan laifuka kusan goma sha biyu wadanda ke da hukuncin dauri na sama da shekaru 100 a gidan yari tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatinta wanda ya haifar da zanga-zangar gama gari, har mutane da dama suka mutu yayin da aka kama wasu masu yawan gaske.