Kotu ta tabbatar wa Habre daurin rai da rai | Labarai | DW | 27.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta tabbatar wa Habre daurin rai da rai

Babu makawa tsohon shugaban kasar Chadi zai shafe tsawon rayuwarsa a kurkuku a cewar kotun musamman ta kasashen Afirka, wacce ta tabbatar da hukuncin da ta yanke a bara bayan da ya daukaka kara.

Kotun musmman ta kasashen Afirka ta tabbatar da hukuncin daurin rai da rai da aka yanke wa tsohon shugaban Chadi Hissene Habre bayan da aka sameshi da laifin kisan kare dangi. Sai dai a lokacin wani zama da ta yi a birnin Dakar na Senegal don saurara karar da ya daukaka, kotun ta wankeshi daga zargin fyade da aka yi masa tun da farko.

Mutane dubu 40 ne suka rasa rayukansu lokacin da Hissene Habre ya tursasa wa al'umma a zamanin mulkinsa daga 1982 zuwa 1990. Tsohon shugaban na Chadi mai shekaru 74 da haihuwa zai yi zaman wakafi a Senegal inda ya samu mafaka bayan da aka hambarar da mulkinsa ko kuma a wata kasa ta daban ta Afirka.

Tun a ranar 30 ga watan Mayun 2010 ne kotu ta daure Habre na iya tsawon ransa tare da tilasta masa biyan tarar miliyan 20 na CFA ga iyalan kowanne daga cikin wadanda ya azabtar ko ya kashe a zamanin mulkinsa.