Kotu ta soke zabe a Malawi
February 3, 2020Talla
Kotun tsarin mulki a Malawin ce dai ta soke zaben kasar da ya bai wa Shugaba Peter Mutharika nasara a watan Mayun shekarar da ta gabata, saboda kura-kuran da ta ce an tafka. Alkalin kotun Healey Potani, ya ce sakamakon hakan dole ne a sake zabe a Malawin.
Manyan 'yan takarar hamayya a zaben kasar ne dai suka kalubalanci nasarar Shugaba Mutahrika, wanda ya sha gabansu da karamin rinjaye.
Kotun ta lura da gyare-gyare kan takardun kada kuri'a da suka fi miliyan daya da budbu 400.
Watanni da dama ne dai aka kwashe ana ta zanga-zanga a Malawin saboda rashin amincewar da aka nuna dangane da sakamakon.