Kotu ta saki tsohon firaministan Pakistan daga fursuna | Labarai | DW | 19.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta saki tsohon firaministan Pakistan daga fursuna

Kotun Pakistan ta bayar da umurnin sakin Nawaz Sharif tsohon firaminista daga gidan fursuna har zuwa lokacin da za a kammala shari'a.

Kotu a kasar Pakistan ta ba da umurnin sakin tsohon Firaminista Nawaz Sharif daga gidan fursuna, tare da dakatar da daurin da aka yi masa na shekaru 10 kan tuhumar cin hanci. Kotun da ke birnin Islamabad babban birnin kasar ta kuma dakatar da hukuncin da aka yi kan 'yar tsohon firaministan da sirikinsa, abin da ake gani zai iya sauya yanayin siyasar kasar.

Kotun ta ce za a saki tsohon Firamnista Nawaz Sharif har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin karshe.

A shekara ta 2016 kormoto kan Panama Papers, lamarin da ya jefa Nawaz Sharif wanda ya yi firamnista sau uku a kasar ta Pakistan, cikin rudani na tuhumar cin hanci da rashawa. abin da ya janyo ya rasa madafun iko tare da jefa shi a fursuna kafin wannan matakin kotun na saki.