1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy zai yi zaman yari

Abdul-raheem Hassan
March 1, 2021

An zargi tsohon shugaban kasar Faransa mai shekaru 66 a duniya kan laifin yunkurin sace bayanan sirri, na wani binciken da wata kotu ke yi a kan badakalar wasu kudade a shekarar 2014.

https://p.dw.com/p/3q3xo
Nicolas Sarkozy Korruption Festnahme
Hoto: Lionel Bonaventure/AFP/GettyImages

Wata kotu a Faransa ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Nicolas Sarkozy hukuncin zaman yari tsawon shekaru uku kan laifin cin hanci da sayer da kayayyakin gwammnati ba bisa ka'ida ba.

Shari'ar na zama irinta na farko da wata kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasa a Faransa kan zargin cin hanci, sai dai akwai yiwuwar Sarkozy zai daukaka kara kan wannan hukunci, duk da cewa hukuncin ya ba shi damar neman sassaucin daurin gida.