1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure Mursi shekaru 20

Mahmud Yaya Azare/USUApril 21, 2015

A kasar Masar kotun manyan laifufuka ta yankewa hambararran shugaban kasar Muhammad Mursi da wasu mukarrabansa daurin shekaru ashirin, kan abin da ta kira laifukan nuna karfi da ta da tarzoma.

https://p.dw.com/p/1DRgq
Ägypten Ansprache Präsident al-Sisi 25.10.2014
Hoto: Reuters/The Egyptian Presidency

Alkalin dai ya tabbatar da cewa ,ba a sami shugaba Mursi din da mukarrabansa da laifukan kashewa ko bada umarnin kashe masu zanga-zanga a fadar mulkinsa da ake kira Qasrul Ittihadiyya ba, kamar yadda akai ta zarginsu a baya a tuhumar, sai dai alkalin ya tabbatar musu da laifin ayyukan dabanci. Inda alkalin ke cewa. “Kotu ta yanke hukuncin shekaru 20 a kan Muhammad Mursi da sauran mukarrabansa, da kuma sanya su karkashin sa idon jami'an tsaro, har na tsawon shekaru 5, saboda aikata laifuffukan nunawa abokan hamayyarsu karfi da tarzoma da kame mutane suna azabtar da su”

Kairo Anhänger von Mursi Protest
Hoto: Reuters


Nan take dai masu adawa da juyin mulki a kasar sukai ta nuna adawarsu da hukuncin suna masu cewa. “Wannan shari'ar girmamawa ce ga Muhammadu Mursi. Wannan rana ce da burinsa ya cika, ya karbi kambun girmamawa daga dubun dubatan Misirawa da ke kaunarsa. Wadanda dominsu ya ki mikawa azzalumai kai bori ya hau. Yau rana ce ta kunyata azzalimai masu fashin mulki“


Shi kuwa, Muhammad Darraj, kusa a kungiyar 'Yan uwa musulmi, siffanta shari'ar ya yi da wasan kwaikwayon da mahukuntan na Masar suka shiryashi, don samun damar ci gaba da tsare Mursi a dokance. “Duk wannan shari'ar shakulatun bangaro ce. Domin Mursi shi ne halataccen shugaba. Kuma kundin tsarin mulki ya fayyace yadda za'a iya yi wa shugaban shari'a. Wannan kotun kuma ba ta bi tsarin ba. Don haka wannan hukuncin da shi da babu duk daya ne”

Ägypten Mursi Urteil
Hoto: AFP/Getty Images


Wasu kuwa a ganinsu, hukuncin da aka yanke mar dimma ya yi kadan. “Duk wanda ya aikata laifi ya zama wajibi a hukunta shi. Hare-haren da yaransa ke kaiwa kan jami'an tsaro da sojoji, dama mutanan gari, ya kai ace an yanke masa hukuncin kisa. Kan banda laifin nuna banbancin da ya yi a lokacin mulkinsa. Yadda babu wani da ake bawa aiki sai 'yan kungiyarsa”


A yanzu haka dai, Mursi din yana dakon wasu hukunce-hukuncen, kan tuhumomi hudu, wadanda suka hada da zargin ba da bayanan asiran gwamnati ga kungiyar Hamas da Hizbullah, wadanda kasar ta sanya su cikin kungiyoyin 'yan ta'adda. Sai kuma zargin fasa gidan yari don sako fursunonin da ke cikinsa.


Tun bayan da shuagaba mai ci Janar Sisi, ya hambarar da Mursi, shekaru biyun da suka gabata, an yanke wa magoya bayan Mursi din sama da dubu hukuncin kisa, cikinsu harda jagoran kungiyar ta 'Yan uwa Musulmi a kasar, Muhammad Badee. A yayin da kotunan kasar suka wanke Husni Mubarak da illahirin mukarrabansa.