1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure Dariye shekaru 14 a kurkuku

June 12, 2018

Bayan tsawon shekaru ana shari'a wata babbar kotu a Abuja ta daure tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye bisa samunsa da laifin Almubazzaranci da cin amanar kasa.

https://p.dw.com/p/2zQGn
Symbolbild Gericht Gesetz Waage und Hammer
Hoto: Fotolia/Sebastian Duda

Wata babbar kotu a Abuja ta daure tsohon gwamman jihar Filato Joshua dariye shekaru 14 a gidan yari bisa samunsa da laifin almubazzaranci da miliyoyin dalolin kudade da aka ware na inganta muhalli.

Da ta ke yanke hukunci mai Adebukola Banjoko ta ce sata da wawashe dukiyar kasa irin wannan ya wushe hankali.

Ta yanke masa shekaru 14 a gidan yari  saboda almubazzaranci da dukiyar kasa da kuma shekaru biyu saboda cin amanannar da aka dora masa.

Dariye ya yi gwamnan Filato a karkashin inuwar 

An zargi tsohon gwamnan da karkatar da kudi fiye da Naira biliyan daya.

Wannan hukuncin na zama na biyu da kotu ta daure tsoffin jami'an gwamnati masu girman mukami.

Makonni biyu da suka wuce kotu ta daure tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame shekaru 14 a gidan yari.