Kotu a Kano ta dakatar binciken Ganduje | Labarai | DW | 05.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Binciken Ganduje ya dauki sabon salo

Kotu a Kano ta dakatar binciken Ganduje

Binciken zargin karbar cin hanci da ake yi wa gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya dauki sabon salo bayan da wata babbar kotu a jihar ta umarci majaliosar dokoki da dakatar da binciken.

Wata babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da majalisar dokokin jihar daga cigaba da binciken da ake yiwa gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje akan zargin karbar nagoro daga hannun 'yan kwangila.

Kotun karkashin jagorancin justice Usman Na Abba, ta bayar da umarnin ne a ranar Talatar nan bayan da wata kungiyar lauyoyi mai rajin kare dimukuradiyya a Najeriya tare da Jagoranta Muhammed Zubair suka shigar da kara domin kalubalantar bincike akan batun na rashawa.

Mai sharia Usman na Abba ya umarci majalisar ta dakatar da binciken har sai an dawo gaban kotun a ranar 12 ga wannan watan na Nuwamba.