Koriya ta Arewa za ta sake wani sabon gwajin Nukiliya | Labarai | DW | 15.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa za ta sake wani sabon gwajin Nukiliya

Jagoran mulkin soji na Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya sanar da cewar ƙasarsa na shirin yin wani sabon gwaji na makaman nukiliya. masu cin dokon zango

Kim Jong Un ya bayyana haka ne a lokaci da ya halarci wani atisaye na gwajin makamai a gabashin ƙasar.Shugabar gwamnatin Koriya ta Kudu Park Geun Hye ta mayar da martani a kan furcin da shugaban na Koriya ta Arewa ya yi, da cewar ya kama hanyar kawo ƙarshen kansa da kansa tun da ya ƙalubalanci ƙasashen duniya.