Koriya ta Arewa ta yi sabon gwajin makami mai lizzami | Labarai | DW | 05.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta yi sabon gwajin makami mai lizzami

Koriya ta Kudu da kawarta ta Amirka sun harba makamai masu lizzami zuwa cikin tekun Japan a matsayin martani ga gwajin wani makami mai lizzami mai cin dogon zango da Koriya ta Arewa ta gudanar a jiya Talata.

Koriya ta Kudu da kawarta ta Amirka sun harba makamai masu lizzami da ke cin gajeren zango zuwa cikin tekun Japan a matsayin martani ga gwajin wani makami mai lizzami mai cin dogon zango da Koriya ta Arewa ta gudanar a jiya Talata.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya bayyana cewa kasarsa ta harba makamin ne a a ranar sallar kasar ta Amirka a matsayin tsarabar barka da salla ga abin da ya kira "shaggun Amirkawa". 

Nasarar harba makamin mai cin dogon zango na a matsayin wani babban ci gaba ga kokarin da Koriya ta Arewar ke yi na mallakar makamin da ke ba ta damar iya harar kasar ta Amirka da makamin nukiliya, wanda ke zama babbar barazana ga tsaron lafiyar kasar ta Amirka. 

A watan Janerun da ya gabata Shugaba Trump na Amirkar ya sha alwashin hana wa Koriya ta Arewar damar mallakar makamin nukiliyar. Sai dai kwararru da dama na ganin makamin d Koriya ta Arewar ta yi nasarar gwajinsa a wannan Talata na iya kaiwa yankin Alaska.