Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami | Labarai | DW | 05.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami

Amirka ta tabbatar da cewar Koriya ta Arewa ta kara yin wani gwajin na makami mai linzami mai cin dogon zango wanda ta harba ya kuma fada a gabar tekun Japan.

Amirka  ta ce makamin na nukiliya samfari KN 15 wanda ka iya cin kamar kilomita 60 na tafiya a karkashin ruwan teku ba shi da wata barazana ga arewacin Amirka.Wannan gwaji dai na zuwa ne daf da lokacin da za a soma wani taro tsakanin Amirka da china, inda za a tattauna batun barazanar da shirin nukiliyar na Koriya ta Arewa  yake da ita ga duniya.