1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami

January 14, 2022

Kasar Koriya ta Arewa ta sake gwajin makamin da ake kyautata zaton makami ne mai linzami duk da irin sukar da kasar ke sha.

https://p.dw.com/p/45WJd
Nordkorea | Raketentest
Hoto: KCNA/KNS/AFP


Hakan dai na zuwa ne sa'o'i kadan bayan Arewan ta soki matakin Amirka na kakaba ma ta sabbin takunkumai a matsayin gargadi ga gwajin da ta yi na baya-bayan nan.

Babban hafsan sojin Koriya ta Kudu ya ce Koriya ta Arewa ta harba wani makami da ba a tantance ba kuma ba ta yi karin haske ba, yayin da masu tsaron gabar ruwan Japan ke cewa bisa dukkan alamu makami ne mai cin dogon zango.

Koriya ta Arewa ta yi ikrarin ingancin harba makamin nata wanda ta ce ta yi ne don tsaronta sai dai kuma Amirka na ta'azzara lamura ta hanyar sake kakaba wasu sabbin takunkumai.