1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka a yankin Koriya

Zulaiha Abubakar
August 16, 2019

Ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Kudu ta sanar da cewar makobciyar ta Koriya Arewa ta harba wasu makamai a tekun da ya hade yankunan biyu a safiyar wannan Juma'a,

https://p.dw.com/p/3NzLA
Nordkorea | Neue Raketentests
Hoto: Reuters/KCNA

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fara tsami ne bayan da shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa, ya zargi takwaransa shugaba Moon Jae-in na Koriya Kudu da yaudara sakamakon wani  atisayen sojoji na hadin gwiwa tsakanin Amirka da Koriya ta Kudun.

Gabanin harba makaman sai da wakilan kwamitin sulhunta kasashen biyu daga bangaren shugaba Kim na Koriya ta Arewa suka  jadadda aniyar kasar ta juya wa shirin inganta alaka tsakanin kasashen baya, wannan dai shi ne karo na shida cikin kankanin lokaci da Koriya ta Arewa ke harba irin wadannan makamai a ci-gaba yi wa makociyar ta ta gargadi.