Koriya ta Arewa ta gayyaci Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 10.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta gayyaci Koriya ta Kudu

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya gayyaci takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in don tattaunawa a birnin Pyongyang.

Südkorea Seoul Treffen von Kim Yo Jong, Ri Son Gwon (picture alliance/AP/Yonhap/K. Ju-sung)

Kim Yo Jong 'yar uwa ga shugaban Koriya ta Arewa na ganawa da abokin tafiya

Kamfanin dillancin labaran Yonhap na Koriya ta Kudu ya bayyana labarin gayyatar a wannan rana ta Asabar da ke zuwa bayan da jami'ai na gwamnatin Koriya ta Arewa suka je kasar ta Koriya ta Kudu don halartar bude bikin wasannin Olympics na lokacin hunturu a birnin Pyeongchang.

Shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu ya gana da manyan jami'ai daga Koriya ta Arewa ciki kuwa har da 'yar uwan shugaban kasar Koriya ta Arewa. Tuni ma dai suka kammala tattaunawar a wannan Asabar kamar yadda fadar shugaban ta nunar, sai dai babu karin haske kan abin da tattaunawar ta kunsa.