1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta nuna wa duniya makamai masu linzami

January 15, 2021

Koriya ta Arewa ta nuna wasu abubuwa da ake tunanin makamai masu linzami ne da aka kera wanda za a iya harbawa daga jiragen ruwan karkashin teku.

https://p.dw.com/p/3nwpU
Nordkorea stellt neue Rakete bei Militärparade vor
Hoto: KCNA/Reuters

Rahotanni sun cewa Koriya ta Arewar ta nuna sabbin makaman yayin wani fareti na sojoji wanda Shugaba Kim Jong Un ya shaida a birnin Pyongyang a wurin bikin kammala taron jam’iyyar da ke mulki wanda ake yi duk bayan shekaru biyar.

Masana ilimin makami sun ce hotunan sabbin makamai masu linzamin da Koriya ta Arewar ta nuna guda hudu sun kasance sabbin samfuri akan wanda ta nuna  a watan Oktobar da ya gabata.

Tun kafin yanzu dai kasar na cikin wasu takunkumi da kasashen duniya suka sanya mata kan kokarinta na ci gaba da mallakar makaman nukiliya da ake ganin ke zama barazana ga zaman lafiyar duniya.