1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta aika wa Amirka sako

January 1, 2019

Shugaba Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa, ya ce yana fatan samun kyakkyawar tattaunawa tsakanin da shugaban Amirka Donald Trump kan abin da ya danganci makamin Nukiliya.

https://p.dw.com/p/3AqKH
Nordkorea  | Neujahrsansprache Kim Jong Un
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/KRT

Shugaba Kim wanda ke kalamai albarkacin shigowar sabuwar shekarar 2019, ya nuna cewa duk da hakan Koriya ta Arewa ba za ta kyale Amirka ta kai ta bango ba.

Ya kuma ce a shirye ya ke ya gana da shugaban na Amirka Mr. Trump a kowane lokacin don cimma matsayar da kasashen duniya za su yi na'am ta ita.

Sai dai ya nanata cewa Koriya ta Arewa na iya komawa ga harbe-harben makamanta muddin Amirkar ta yi garajen bayyana wani takunkumi a kanta.

Cikin watannin da suka gabata ne Koriyar ta zargi Amirka da gaza cimma bukatun da suka amince da su kan batun rusa cibiyar gwaje-gwajen makaman nukiliyar kasar da ma na masu linzami.